Tinubu ya amince da gina jami’ar tarayya a Kudancin Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya amince da buƙatar samar da jami’ar tarayya a Kudancin Jihar Kaduna, kamar yadda Mataimakinsa, Kashim Shettima ya faɗa.

Shettima ya bayyana hakan a lokacin da ya je gaisuwar ta’aziyyar rasuwar Agwom Akulu na Masarautar Ikulu wanda kuma ɗan uwa ne ga Bishop Matthew Hassan Kuka.

Ya kuma ce ana tattaunawa game da samar da asibitin tarayya (Federal Medical Center) a Kafanchan dake Kudancin jihar.

Ya jaddada ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Tinubu na samar da ci-gaba ga yankin, yana mai bada misali da naɗa Janar Christopher Musa a matsayin Babban Hafsan Tsaron Nijeriya la’akari da yanayin tsaro a shiyyar arewa.

Ya kuma yaba wa Gwamna Uba Sani na jihar bisa ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wa al’umma, ya na mai cewa Gwamnatin Tarayya za su haɗa hannu da ita wajen tabbatar da ƙaddamar da ababen more rayuwa a Kudancin Kaduna.

By Babaji