Jigon APC ya yaba wa sarkin Ondo kan bada sarautar gargajiya ga ɗan Majalisar Wakilan Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jigo a jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara kuma tsohon mai baiwa gwamnan Jihar Zamfara shawara kan harkokin kasuwanci da gudanar da kasuwanci Suleiman Usman Zumunchi, ya yabawa mai martaba Sarkin Jihar Ondo, Oba Akadri Saliu Momoh kan bada sarautar gargajiya ga Ɗan Majalisar Wakilai Abdulmalik Zubairu, a matsayin “Cif Mayegun of Ikare-Akoko Kingdom”

Zumunchi ya bayyana haka ga manema labarai a Gusau a ranar Litinin.

Ya bayyana ɗan majalisar tarayya a matsayin shugaba marar gajiyawa kuma wanda ya sadaukar da kansa wajen sanya farin ciki ba kawai ga al’ummarsa ba har ma da ɗaukacin al’ummar Zamfara.

Zumunchi, ya bayyana bayar da sarautar gargajiyar a matsayin abin da ya dace, inda ya nuna cewa mai martaba (Hon. Zannan Bungudu) haziƙi ne da ya taka rawar gani a kowane fanni na rayuwa, don haka akwai buƙatar a ba da irin wannan muƙami gareshi.

A cewarsa, wannan karramawa da aka yi a Jihar Ondo wata alama ce da ke nuna irin gudummawar da ɗan majalisar tarayya ke bayar wa wajen cigaban al’umma.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne Oba Akadri Saliu Momoh Olukare na Ikare-Akoko dake jihar Ondo, ya ba ɗan majalisar wakilan mai wakiltar mazabar Maru/Bungudu, Hon. Abdulmalik Zubairu (Zannan Bungudu), sarautar gargajiya a matsayin “Chief Mayegun of Ikare-Akoko Kingdom.

Hakazalika Zumunci ya ci gaba da cewa, sarautar ” Cif Mayegun na mulkin Ikare- Akoko” da Mai Martaba Oba Akadri Saliu Momoh ya baiwa Abdulmalik Zanna, ya nuna irin yadda al’ummar Kudu da Arewa ke da alaƙa da juna.

Ya yaba da irin rawar da ɗan majalisar ya nuna sannan ya buƙace shi da ya ɗore da kyakkyawan salon wakilin shi.

“Ina tare da kai Hon. Abdulmalik Zubairu wajen miƙa godiyata ga Mai Martaba Oba Akadri Saliu Momoh, da ya ba ka muƙami wanda ɗaya ne daga cikin muhimman muƙamai a masarautar Jihar ta Ondo”. Zumunchi yace.

By ukarofi