Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta jaddada ƙudirinta na gudanar da ayyukan haɗin gwiwa da sintiri tare da sojojin Nijar duk da ƙazafin da shugaban sojojin Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ya yi wa Nijeriya.
Wannan dai na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda kamar Lakurawa a yankin Arewa maso Yamma da sauran ’yan ta’adda a sassan jihohin da ke kan iyaka tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.
A baya-bayan nan Tchiani ya zargi Nijeriya da kyale Faransa ta yi amfani da yankinta a matsayin matattarar hargitsa ƙasarsa.
Ya kuma yi zargin cewa gwamnatin Faransa ta bai wa Nijeriya kuɗaɗen da za ta kafa sansanin soji a jihar Borno.
“Faransa har ma ta yi tayin bayar da kuɗi ga hukumomin Nijeriya don kafa sansani a jihar Borno, da nufin tada zaune tsaye a ƙasashenmu,” inji Tchiani.
“Mun sanar da hukumomin Nijeriya da suka haɗa da Nuhu Ribadu da Ahmed Abubakar Rufa’i game da wani gagarumin maƙarƙashiya na hargitsa ƙasar Nijar.
“Dajin Gaba, wanda ke kan iyakar Sakkwato (Nijeriya) da Nijar, ’yan ta’adda ne da Faransa da ISWAP suka ɗauka a matsayin sansaninsu. Abin takaici, da alama mun zaɓi waɗanda za mu tattauna da su da kyau, saboda kwarewarsu da Faransa ta yi amfani da su wajen lalata iyakokin Nijar da Nijeriya da Benin da Burkina Faso,” inji Tchiani yana cewa.
A martanin da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya mayar, ya yi watsi da zargin.
Da aka tambaye shi ko Nijeriya za ta janye daga shirinta na tsaron haɗin gwiwa da jamhuriyar Nijar, Daraktan ayyukan yaɗa labarai na tsaron Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba, ya ce duk da wannan ƙazafi, sojojin Nijeriya za su ci gaba da gudanar da ayyuka tare da takwarorinsu na Nijar.
“Sojoji za su ci gaba da yin sintiri tare da aiki tare da sojojin Nijar,” inji Buba.
Da yake magana game da matakin da sojojin suka ɗauka, Kwamandan Pioneer, masu aikin sintiri na hazin gwiwa tsakanin Nijeriya da Nijar, ya ce, CP Rabiu Ladodo (mai ritaya) ya bayyana cewa wasu muhimman batutuwa guda biyu – tsaro da walwalar jama’a a Nijeriya da Jamhuriyar Nijar – ba za a taɓa yin kasa a gwiwa ba saboda zurfafa alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.
Ya kuma jaddada cewa, mafita ɗaya tilo da za a magance ƙalubalen tsaron da suke fuskanta shi ne a haɗa kai da juna.
