Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban kasuwar Galadima, Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya bayyana damuwarsa akan yadda masu sayar da man girki a tsakanin al’umma musamman a unguwanni ba sa rage farashin man, alhali kuwa an ɗan samu sauƙi akan ta’azzarar tsada da ya yi a kwanakin baya.
Da yake zantawa da manema labarai ya ce kowa ya sani a watannin baya da suka gabata an samu hauhawar tsadar man girki, amma cikin ikon Allah yanzu Allah ya juya lamarin ana samun sauƙi da ya fi a ce ƙaruwa yake a harkar mai an samu ragi.
Ya ce amma yana mamaki wani ya ce mai bai rage kuɗi ba, ya rage kuɗi tunda jarkar man da ya kai N95,000 a baya gashi yanzu baya wuce N82,000 zuwa 83,000 aƙalla an sami sauƙin N15,000 ko da N10,000 an samu sauƙi akan yanda yake da. Ai ko ba za a ce ba a samu sauƙi ba.
Ya ce illa iyaka dai yana jin labarin cewa wai a cikin gari mutane da suke sayarwa jama’a ba su rage ba, amma a gaskiya su a kasuwa sun rage an sami sauƙi ba a cigaba da samun hauhawar yanzu sauka ma ake samu na kayan.
Alhaji Mustapha Shu’aibu ya yi kira ga dukkanin jama’a masu sayar da mai a cikin gari yadda suma suka sami sauƙi su ragewa jama’a Allah ya kawo rahama, ba tasu ba ce su kaɗai ta kowa da kowa ce, domin sanda aka yi tsadar nan kowa ya bi tsadar nan, an sha wuya to yanzu an samu ɗan sauƙi komai ƙanƙantar yanda aka rage suma su rage aƙalla kowace kwalba ace an ragewa mutane N250 mutane za su san cewa an samu sauƙi.
