Bafarawa ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki a kan Turji

Spread the love

Daga SANI HAMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa a kan Turji.

“Gwamnati ta ɗauki barazanar Turji da muhimmanci kuma ta kare al’umma,” inji Bafarawa.

“Muna buƙatar zaman lafiya don magance matsalolin yunwa da rashin aikin yi, amma dole ne a haɗa hannu don tallafa wa jami’an tsaro.”

A halin yanzu, sojoji sun bayyana Bello Turji a matsayin “wanda ya kusa zuwa hannu” tare da alƙawarin kawar da shi.

A cewar Manjo Janar Buba, “Sojoji suna ƙara matsa lamba a kan ‘yan ta’adda.

“Turji zai gamu da irin abin da shugabannin ’yan ta’adda da dama suka fuskanta a wannan shekarar.

“Sojoji sun ƙuduri aniyar kare ’yan Nijeriya daga waɗannan bata-gari.”

By ukarofi