Kasafin 2025: An shawarci gwamnati ta yi amfani da biliyan N113 a raya ƙasa maimakon sayen motoci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani masani kan harkokin kuɗi, Farfesa Uche Uwaleke, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta karkatar da Naira Biliyan 113 da aka tanadar a cikin ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 na sayen motoci zuwa ayyukan samar da ababen more rayuwa a ƙasar.

Uwaleke, farfesa ne a fannin kasuwar jari, kuma shi ne Daraktan Cibiyar Nazarin Kasuwar Hannu a Jami’ar Jihar Nasarawa Keffi.

Ya bayar da shawarar ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce, ya tattara jerin sunayen hukumomin gwamnati 288 da suke jerar sayen motoci a cikin kasafin ƙudinsu na shekarar 2025.

A cewarsa, waɗannan motocin za a shigo da su ne daga ƙasashen waje don haka yana da tasiri ga farashin canji.

Ya ce, ya kamata shugabannin hukumomin su ɗage waɗannan sayayyar har zuwa shekarar 2026.

“Za a iya ba da adadi mai yawa zuwa wani aiki wanda aka tsara don haɓaka kayan aiki da rage hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi.

“Misali, ana iya amfani da kudin wajen fara aikin Gwamnatin Tarayya, tare da gwamnatocin jihohi.

“Irin wannan aikin ya kamata a san shi da ‘ Gundumar Daya; Aikin Samfura ɗaya (ODOP) a kowace gundumomi 109 na Sanata, inda kowace gunduma ta samu aƙalla Naira biliyan ɗaya.

“Haka kuma za a iya amfani da ita wajen farfaɗo da ‘ƙaramar Hukuma ɗaya; Aikin Samfura ɗaya (OLOP), wanda bai taɓa yin wani tasiri mai mahimmanci ba saboda rashin kulawa,” inji shi.

Ya ce, a yanayi na biyu kowace ƙaramar hukuma za ta iya samun aƙalla Naira miliyan 145 daga cikin kuɗaɗen da za a kwato sakamakon tsaikon da aka yi na sayen motoci.

By ukarofi