Daga USMAN KAROFI
Hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa NCDC ta fitar da wata sanarwa domin wayar da kan jama’a da ɗaukar matakan kariya kan barazanar cutar Human Metapneumovirus (HMPV).
Wannan na zuwa ne sakamakon rahotanni daga ƙasashen Sin, Birtaniya, da wasu sassa na duniya da ke nuna ƙaruwar yawan masu kamuwa da cutar.
HMPV wata cuta ce ta numfashi da ke haifar da alamun mura mai sauƙi har zuwa matsanancin ciwon numfashi, musamman ga ƙananan yara, tsofaffi, da masu ƙarancin garkuwar jiki.
HMPV na yaduwa ta hanyar fitar iska daga hanci ko baki, cuɗanya da mai ɗauke da cutar, ko kuma ta hanyar taba wurare da ke ɗauke da ƙwayar cutar.
Duk da cewa ba a sami rahoton ƙaruwar yawan masu cutar HMPV a Najeriya ba, NCDC ta bayyana bukatar yin taka-tsantsan. Ta kuma ce tsarin lura da cututtuka na National Influenza Sentinel Surveillance (NISS) da ke bibiyar cututtukan numfashi kamar ILI da SARI yana ci gaba da bayar da bayanai cikin lokaci domin gano duk wata barazana.
Don ƙarfafa shirin yaƙi da wannan cuta, NCDC ta ƙara faɗin tsarin gwaji don gano HMPV cikin sauri. An haɗa gwajin HMPV cikin tsarin NISS da ake amfani da shi wajen gwajin korona.
Haka kuma, an ba da umarni ga ɗakunan gwaje-gwaje a jihohin da ke da filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa su kasance masu shirin gudanar da gwaje-gwaje cikin hanzari in hakan ta taso.
NCDC ta kuma fara aiki tare da jihohi wajen horas da ma’aikatan lafiya kan yadda za a kula da waɗanda suka kamu da cutar, tare da samar da wuraren killace masu cutar idan buƙatar hakan ta taso.
A ƙarshe, NCDC ta yi kira ga al’umma su rika wanke hannuwa akai-akai da sabulu da ruwa mai tsafta, su rufe baki da hanci idan suna tari ko atishawa, su kuma kauce wa cunkoso musamman ga yara da tsofaffi. Ta kuma yi gargaɗin gujewa yaɗa jita-jita tare da amfani da bayanai daga kafofin hukumar. Duk wanda ya ji alamun cutar, kamar mura, tari, zazzabi, ko wahalar numfashi, an shawarce shi da ya nemi kulawar likita ba tare da bata lokaci ba ko kuma ya kira lambar hukumar 6232.
