Ɗan sandan da aka karrama saboda ƙin karɓar cin-hancin $200,000, Daniel Amah ya musulunta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin kwamishinan ƴan sanda, Daniel Amah da ya shahara saboda ƙin amincewa da karɓar cin-hanci na Dala 200,000 ya karɓi addinin Musulunci a yayin wani biki da aka gudanar a Fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

A yayin bikin ne, wanda aka gudanar a ranar Talata, an marabci ɗan sandan cikin karamci inda ya zaɓi da ya sauya sunansa zuwa Muhammad.

A lokacin da ya ke magana, Sarki Sanusi ya yi kira ga jami’in da ya nemi ilimin addinin musulunci tare da kiyaye salloli biyar a kowacce rana da sauran shika-shikan Muslunci.

Ya kuma yi masa fatan zama ɗaya daga cikin nagartattun Musulmai a duniya, yana mai kira a gare shi da ya cigaba da ayyukansa na gari tare da ƙoƙarin sauke haƙƙoƙin iyayensa ba tare da la’akari da addininsu ba.

A watan Afrilun 2022 ne aka karrama Amah bayan ya ƙi karɓar cin-hancin maƙudan kuɗaɗen daga wasu da ake zargi da fashi da makami sakamakon satar kimanin Naira miliyan 300 a yayin wani fashi.

Babban wanda ake zargin mai suna Ali Zaki, ya shirya ne da ƴan fashi don yi fashi wa wani ɗan harkar canji dake ɗauke da tsabar kuɗi na Dala 750,000.

Ganin nagartar ɗan sandan ne yasa Hukumar kula da harkokin ƴan sanda ta PSC ta ƙara wa jami’in matsayi daga CSP zuwa ACP a Nuwamban 2022.

Haka ma tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya karrama shi da kyautar nagartaccen ma’aikacin al’umma biyo bayan yabo da ya samu daga Shugaban Hukumar hana Rashawa da Laifuka masu kama da ita ta ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye.

By ukarofi