NUJ ta koka kan yadda ake yanken lantarki ba bisa ƙa’ida ba a Bauchi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), reshen Jihar Bauchi, ta yi Allah-wadai da yadda Kamfanin Rarraba Wutar Lantarkin na Jos (JED) ke yanke-yanken wuta a jihar Bauchi ba tare da ƙaƙƙautawa ba.

Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun sakataren ƙungiyar, Isah Garba ya bayyana rashin jin daɗinta kan yadda jami’an JED ke gudanar da aikin yankar wuta da ba ta dace ba musamman ga kwastomomin da ke aiki da mitar da aka riga aka biya, don kawai tilasta wa kwastomomin su dawo biyan kuɗaɗen da aka caje su.

Ya ce, ƙungiyar ta lura da cewa akwai cuwa-cuwa wajen biyan kuɗin wutar lantarki.

“ƙungiyar ta caccaki ayyukan wasu jami’an JED waɗanda ke damun abokan cinikinsu da gangan har ma da waɗanda ke aiki da mita da aka riga aka biya, kawai don tilasta musu biyan kuɗaɗen da aka kiyasta.

“NUJ ta jihar Bauchi ta shawarci gwamnatin jihar Bauchi da ma’aikatu da hukumomin jihar da su nemi hanyar samar da wutar lantarki, ta yadda za su yi tanadi mai yawa daga wasu maƙudan kuɗaɗe da ake caja duk wata.

Sanarwar ta ƙara da, “NUJ ta yi kira ga mahukuntan JED da su riƙa sanya kwararrun ma’aikatan da ke da kyakkyawar alaƙa da kwastomomi don ba su damar samar da ingantattun ayyuka ga kwastomominsu.”

By ukarofi