Sojoji sun nemi goyon bayan ƴan jarida wajen yaƙi da ta’addanci a Katsina

Spread the love

Daga Umar Garba a Katsina

Rundunar sojojin Najeriya ta 17 da ke Katsina ta yi kira ga ‘yan jarida da su ba da goyon bayansu wajen yaqi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro a jihar.

Kwamandan rundunar a Katsina Birgediya Janar, Babatunde Omopariola ne ya yi wannan kira a lokacin wata liyafar cin abinci da qungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) a reshen jihar Katsina.

An gudanar da taron ne da nufin qara qarfafa hadxin gwiwa tsakanin sojoji da kafafen yaxa labarai wajen magance matsalolin tsaro da yankin ke fuskanta.

“Ya kamata a bada fifiko ga ci-gaban aikin jarida don magance matsalar rashin tsaro yadda ya kamata”, inji Omopariola.

“Kafofin yaɗa labarai na taka muhimmiyar rawa a kullum wajen daidaita ra’ayoyin jama’a wanda kan iya yin tasiri kan ayyukan soji. Ta hanyar yin aiki tare, za mu iya samun goyon bayan jama’a a wannan lokaci na yaxa labarai.”

Ya bada shawarar sanya ‘yan jarida cikin tsarawa da aiwatar da ayyukan soji don daƙile bayanan ƙarya tare da samar da ingantattun rahotanni.

Ya ce “Wannan zai taimaka matuƙa wajen duba munanan rahotanni game da ayyukan hukumomin tsaro. Har’ilayau, ya samar da wata kafa ta ƙarfafa abokantakar sojoji da kafafen yaɗa labarai da kuma ɗinke ɓarakar da ke tsakaninmu.”

Ya kuma buƙaci ‘yan jarida da su cigaba da nuna kishin ƙasa a cikin rahotannin da suke bayarwa tare da kauce wa abubuwan da ka iya cutar da tsaron ƙasa.

A nasa jawabin, shugaban NUJ reshen Katsina, Tukur Ɗan-Ali, ya nuna jin daɗinsa bisa kyakkyawar tarbar da rundunar ta yi wa ƙungiyar.

Ya ce, “A kowane lokaci mun yi alƙawarin amsa kiran rundunar soji da kuma samar da ƙwarewar watsa labarai a duk lokacin da ake buƙata.”

Ya ƙara da cewa “ƴan jarida a Katsina za su cigaba da haɗa kai da rundunar soji da sauran jami’an tsaro don inganta haɗin-gwiwa tsakaninsu da jami’an tsaron ƙasa”, inji Ɗan-Ali.

By ukarofi