Rikicin Masarautar Kano: Ɗan’Agundi ya garzaya Kotun Ƙoli

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Alhaji Aminu Ɗan’Agundi, wanda ɗaya ne daga cikin masu zaɓen sarki a ɓangaren Sarki Aminu Ado da babban lauyan da ke kare ɓangarensu, sun ƙudiri aniyar ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli game da hukuncin da Kotun Ɗaukaka ƙara ta yi akan shari’ar sarautar Masarautar Kano.

A yayin hukuncinta, Kotun Ɗaukaka ƙara ta ce Babbar Kotun Tarayya ba ta da ikon shiga cikin rikicin Masarautar, wanda gwamnatin jihar take maraba da shi.

Antoni-Janar kuma Ministan Shari’a na Kano, Haruna Dederi ya ce hukuncin ya tabbatar da matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka na fayyace bayanai game da harkokin shari’ar masarautu da kuma iyakance kotunan da ke da hurumin sauron ire-iren ƙararrakin da suka shafe su.

Saidai, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, Ɗan’Agundi ya ce ya umurci tawagarsa ta shari’a da ta shirya ɗaukaka ƙara game da hukuncin da Kotun Ɗaukaka ƙara ta yi a Kotun Ƙolin.

Ya ce akwai kurakurai game da bayyana hukuncin daga ɓangaren gwamnati, wadda take goyon bayan Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin.

Ɗan’Agundi ya ce ba daidai ba ne Kotun Ɗaukaka ƙara ta ambaci shari’ar a matsayin ta sarauta a madadin ta tauye haƙƙin ɗan-adam.

Ya ƙara da cewa, ba wai ya na ƙalubalantar ƙarfin doka ta Majalisar Dokokin jihar ko ƙoƙarin samar da gyara ba ne, ya ce amma ba a bi hanyoyin da dokar Majalisar Masarautar Kano ta 2024 ta tsara ba.

Har’ilayau, Ɗan’Agundi ya koka da cewa, a matsayinsa na ɗaya daga cikin masu zaɓen Sarki, ba a girmama shi ba a lokacin da aka soke dokar majalisar masarauta ta 2024.

A halin yanzu, al’umma tana jira don jin hukuncin da Kotun Ƙoli za ta yanke game da shari’ar.

By ukarofi