Gwamnatin Tarayya ta sake bada kwangilar aikin titin Abuja zuwa Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa an sake baiwa kamfanin Infoƙuest Nigeria Limited kwangilar ɓangaren da aka soke na babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.

Idan dai ba a manta ba, gwamnati ta soke kwangilar sashe na biyu na hanyar da ta haɗa Abuja zuwa Kaduna daga kamfanin Julius Berger Construction saboda taƙaddamar farashin kwangila.

Da yake jawabi a lokacin da yake duba aikin hanyar, Ministan Ayyuka, Daɓid Umahi, ya ce an bai wa kamfanin kwangilar ne bayan da ma’aikatar ta samu batun ‘No Ojection’ daga Hukumar Kula da Kayayyakin Jama’a ta N252.89 kuma za ta gabatar da kwangilar don amincewa a zama na gaba na Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Yayin da ya ke bayyana dalilin da ya sa aka soke kwangilar wannan sashe daga hannun Julius Berger, Ministan Ayyuka, Sanata Daɓid Umahi, ya ce Julius Berger Plc ya rage saurin aiki a wurin tare da rubuta wasika ga ma’aikatar ayyuka ta tarayya inda ta buƙaci a sake duba biliyan N797 zuwa N797, tiriliyan N1.5 wanda ke nuna ƙaruwar kashi 88.21. Adadin da gwamnatin tarayya ba ta son biya.

Ya ce, bayan da aka dawo da baya, an yi amfani da tsarin tantancewar wanda aka gayyaci ‘yan kwangila guda shida da suka haɗa da Julius Berger Plc don yin takara.

A cewarsa, ‘yan kwangilar guda shida sune kamar haka: M/s Julius Berger Nig. Plc, M/s Hitech Construction Company Limited, M/s Infoƙuest Nigeria Limited, M/s CBC Nigeria Limited, M/s CCECC Nigeria Limited da M/s CGC Nigeria Limited.

“Ina mai farin cikin sanar da cewa kamar yadda ya faru a, mun samu “No Objection” daga BPP kan kuɗi naira biliyan 252.89 na kwangila kuma ina da tabbacin FEC za ta ba mu amincewa a zama na gaba amma bari in ce mun ƙara da cewa kilomita 10.6 a kan titin Kano don kai aikin zuwa filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano kuma mun kara da wani kilomita 5 zuwa Kogi da kuma cikakken sanya hasken rana don shirya gaba daya titin don aiki da kuma gyara,” inji shi.

By ukarofi