Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta cafke wasu mutane shida da ake zargi da laifin garkuwa da mutane da fashi da makami, tare da ƙwato shanu 50 da aka sace.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan ya fitar, an kama mutanen ne a yayin gudanar da ayyukan hadin gwiwa da aka gudanar a ranakun 19 da 20 ga watan Janairu, 2025, biyo bayan sahihan bayanan sirri.
A farmakin farko da aka kai a ranar 19 ga watan Janairu, jami’an ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin DPO na Samaru-Zariya sun kai samame a maboyar Zango da Hayin Jarumai.
An kama mutane hudu Abubakar Alkamu (29), Ahmed Shaibu Lama (24), Hassan Isah (25), da Umar Abubakar (25). An gano wata wuka da aka ce an yi amfani da su wajen aikata laifin, daga gidan ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin.
Waɗanda ake zargin sun amsa laifin su a wasu ayyukan fashi da makami. Ana ci gaba da ƙoƙarin kamo sauran mambobin ƙungiyar, ciki har da shugabanninta, waɗanda akwai hannunsu, inji PPRO.
Hassan ya kuma bayyana cewa, wani samame da DPO na Jere ya jagoranta, an kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne: Abubakar Ahmadu, dan asalin Mayo Belwa, da Shehu (wanda ba a san sunan su ba) daga Tango, dukkansu a jihar Adamawa.
“Rundunar ‘yan sanda ta kwato wayoyin hannu uku da N158,600 daga hannun waɗanda ake zargin, wadanda suka amince da cewa suna cikin kungiyar ‘yan bindiga da suka yi ƙaurin suna wajen ta’addancin babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna. An ƙaddamar da farautar waɗanda suka yi garkuwa da su.
“A wani lamari na daban da ya faru a safiyar ranar 20 ga watan Janairu, ‘yan sanda sun amsa kiran da aka yi musu na nuna bacin ransu game da harin da aka kai a ƙauyen Dandako, inda aka sace shanu 50. Jami’an sashin Hunkuyi sun bi sawun wadanda ake zargin har kauyen Marke, inda suka yi ta harbe-harbe. ƙarfin wutar da ‘yan sanda ke da shi ya tilasta wa waɗanda ake zargin yin watsi da shanun suka gudu zuwa cikin daji. Ana ci gaba da ƙoƙarin zaƙulo ɓarayin da suka tsere.
“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Rabi’u Muhammad, ya yaba wa jami’an kan ƙwazonsu da bajintarsu. Ya nanata ƙudurin rundunar na yin aiki tare da sojoji, sauran jami’an tsaro, da al’ummomin yankin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
“Kwamishinan ‘yan sandan ya buƙaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da kai rahoto ga ‘yan sanda abubuwan da ake zargi, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kan al’umma wajen magance miyagun laifuka,” inji kakakin ‘yan sandan.
