Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar Anthrax a Zamfara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ma’aikatar Kula da Daddobi ta Nijeriya ta yi kira ga ’yan Nijeriya da su kasance cikin shiri bayan tabbatar da ɓullar cutar Anthraɗ a Jihar Zamfara.

A wata sanarwa da daraktan watsa labarai na ma’aikatar, Ben Goong ya fitar, ya ce akwai buƙatar a ƙara ƙaimi wajen lura domin rage yaɗuwa da rage illar cutar.

Anthraɗ, cuta ce da ƙwayar cutar ‘bacterium Bacillus anthracis’ ke jawowa, kuma tana kama dabbobi irin su shanu da awakai da sauran su, sannan tana kama mutane musamman idan sun yi mu’amala da dabbobin da ke ɗauke da cutar ko kuma suka sha abin da dabbobin ke samarwa.

Daga cikin alamomin cutar akwai zazzaɓi da tari da amai da bushewar maƙogwaro da ciwon kai da ƙaiƙayi da sauran su.

“Duk da cewa akwai rigakafi da ake yi wa dabbobi domin kare yaɗuwar cutar, ganowa ta cikin sauri da ɗaukar matakan da suka dace ya fi kyau da saurin daƙile ta.

“Don haka ne muke kira da mutane musamman a jihohin da suke da maƙwabtaka da jihar Zamfara da su ɗauki matakan kariya da ɗaukar hanyoyin domin daƙile yaɗuwarta.”

By ukarofi