Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya tabbatar wa mambobin ƙungiyar matasa ƴan hidimar ƙasa Karo na 2024 batch C, stream 11 da aka turo Jihar Zamfara, ƙudurin gwamnatin sa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu a tsawon watanni tara da zasu yi aikin bautar ƙasa a jihar.
Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a wajen bikin rantsar da sabbin masu yi wa ƙasa hidima na rukunin (batch C) na shekarar 2024 (stream 11) da aka tura Jihar a sansanin horar da masu yi wa ƙasa hidima na wucin gadi da ke Gusau a yau ranar Juma’a.
A cewarsa, Jihar na fuskantar matsalar rashin tsaro sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda na ‘yan bindiga, yana mai jaddada cewa sannu a hankali zaman lafiya yana dawowa domin gwamnatin sa za ta samar da dukkanin hanyoyin da suka dace don tabbatar da kyakkyawan yanayi ga masu yiwa Ƙasa hidimar domin gudanar da ayyukan su na bautar ƙasa cikin lumana da nasara.
Ya buƙace su da su yi amfani da ilimin da suke da shi wajen haɓaka tattalin arzikin jihar da ci gaban jihar a tsawon zaman su a jihar.
Gwamna Dauda ya kuma buƙaci ’yan ƙungiyar yiwa Ƙasa hidimar dasu guji duk wani abu na rashin ɗa’a da zubar da mutuncin su a zamantakewar su da zai iya cutar da su da kuma shafar aikin su na yiwa Ƙasa hidima a jihar.
“Zamu tabbatar da tsaro da jin daɗin ku a lokacin da kuke gudanar da ayyukan yiwa Ƙasa hidima a jihar, kuma na buƙace ku da ku kasance jakadu nagari, ku nisanci duk wani nau’i na rashin bin doka da oda da kuma amfani da ilimin ku wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikin jihar”. Gwamna Dauda ya bayyana
A nasa jawabin, kodinetan NYSC na jiha, Mallam Muhammad Lawan Ahmad ya bayyana cewa shirin na NYSC yana ƙunshe da shirye-shirye guda huɗu.
“Wannan shirin horarwa ana yin shine don baiwa membobin wadatar muhalli, zamantakewa, jagoranci da kuma ƙwarewar aiki Hidima”. Yace
Ya kuma ƙara da cewa, a yayin da ake gudanar da shirin horarwar, za a gabatar da laccoci na gargajiya/al’adun da suka shafi jihar, shirye-shiryen zama ‘yan ƙasa da na shugabanci, horo, koyon sana’o’i da dai sauransu.
“A ƙarshen wannan horaswa, abin da muke sa rai shi ne, zai sauya tunanin waɗannan mambobin ƙungiyar masu yiwa Ƙasa hidima don cigaba da gudanar da ayyukan su na bautar ƙasa da kuma kishin ƙasa a tsakanin su”. Ya ƙara da cewa
Ko’odinetan ya kuma buƙaci ’yan bautar ƙasar da su cigaba da ɗa’a da juriya da kuma fahimtar mahimmin kwas din da za’a horar dasu.
“Hakazalika, ina ƙalubalantar ku daku himmatu wajen banbance kanku tun daga sansani, kuma kada ku kasance masu sa ido, kuyi cuɗanya da abokan aikinku, ku ba da himma a duk ayyukan sansanin da bayar da gudummawar Ku yadda ya kamata don samun nasarar da akasa a gaba”.
