
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sandan Kano ta aika da saƙon ankarar da al’umma bayan samun wasu rahotonnin sirri game da wani shirin ta’addanci da ake zargin wasu ɓata-gari sun shirya don farmakar wuraren haɗuwar mutane a jihar.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, an yi kira ga al’umma da su ƙaurace wa wuraren taruka da kuma kula da abubuwan da ke kai-kawo a yankunansu.
Hakan wani salo ne da zai taimaka wa jami’an ƴan sandan wajen daƙile shirin ƴan ta’addar.
Ya kuma ce an baza jami’ain kula da abubuwa masu fashewa a wasu ɓangarori da aka ware a jihar.
Haka kuma ana kira ga al’umma da su kasance masu ruwaito dukkan wani abin zargi da suka gani a yankunansu ga ofishin ƴan sanda mafi kusa da su don tabbatar da tsaro a gare su.
Kazalika, rundunar ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankulansu gami da sanya ido a unguwanninsu, ta na mai godiya da irin goyon bayan da take samu daga gare su.
