Majinyata a Asibitin Tarayya na Keffi sun yaba wa Dr. Adamu

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Majinyata da iyalansu da ke tare da su a yayin da suke karɓar magunguna a babbar cibiyar nan ta magunguna na gwamnatin tarayya da ake kira Federal Medical Centre (FMC) a Turance dake garin Keffi a jihar Nasarawa, sun yaba wa babban daraktan cibiyar Dokta Yahaya Baba Adamu dangane da tsarinsa na tabbatar majinyatan na samun cikakken kulawa a yayin da suke kwanciyar jinya a cibiyar.

Masu jinyar sun bayyana haka ne a lokacin wata ziyarar neman rahoto na musamman da wakilinmu a jihar ta Nasarawa ya kai cibiyar inda ya gana da su ɗaya bayan ɗaya game da yanayin kulawa da suke samu daga likitoci da sauran ma’aikatan cibiyar, inda suka tabbatar cewa tabbas suna samun kulawa da ƙauna da ma lallashi wajen waɗanda ke kula da ciwon nasu daban-daban.

A cewarsu dole ne su yaba wa babban daraktan cibiyar Dokta Yahaya Baba Adamu don tun zuwansa shugabancin cibiyar lafiyar ta FMC ne abubuwa suka canja musamman a fannin dangantaka dake tsakaninsu dake jinyar da waɗanda suke kula da su don ada kafin zuwan sa (Dr, Yahaya Baba Adamu) anyi ta samun rashin jituwa tsakanin su da likitoti da sauran ma’aikatan cibiyar sakamakon rashin kulawa daya dace ayi musu inda a wasu lokutan ma acewar su hakan yana kai ga rasa rai ko karin ciwon da sauran su amma a yanzu hakan ya zama tarihi sakamakon tsarin na Dr. Yahaya Baba Adamu.

Majinyatan da aka zanta da sun duk sun kara da cewa daga cikin abinda babban daraktan cibiyar dokta Yahaya Baba Adamu keyi a fannin shine bayan ganawar musamman da yake yi da likitotin akai-akai game da bukatar rika kulawa da majinyatan yadda yadace yakan kuma samu lokaci da kansa yana zagawa kowanna dakin jinya daya bayan daya don tabbatar masu kula da sun suna bin umurnin sa’anan duk likita ko ma’aikaci da aka kama da laifin wulakanta majinyatan nan take hukumar gudanarwar cibiyar bata wata-wata wajen hukinta shi ko ita bayan bincike ya tabbatar da hakan.

Dangane da yanayin nahurori da sauran kayayyakin aiki da ake amfani dasu a wajen kulawa dasu a cibiyar majinyatan duk sun sake yaba wa cibiyar karkashin jagorancin Dr, Yahaya Baba Adamu game da ingancin nahurorin wadanda suka kwatanta su cewa sunyi daidai da zamani kana ana samun isheshen wutar lantarki da ruwa da kuma tsaptaceccen muhallin da sauran su da hakan acewar su yana taimaka matuka wajen samun saukin su cikin sauri sabanin yadda lamarin yake a da.

A karshe sai suka yi amfani da damar inda suka bukaci cibiyar ta magungunan ta cigaba da wannan sadaukarwa don Allah ne kadai zai biya su gobe kiyama.

Binciken wakilin namu dai ya gano cewa kafin zuwan babban daraktan cibiyar ta FMC na yanzu wato Dr, Yahaya Baba Adamu anyi ta samun mummunar sabani tsakanin bangarorin biyu wato majinyata da likitoti dake kulawa dasu da har lamarin yakan kai ga ba hamata iska aga jami’an tsaro suna shigowa don kwantar da tanzomar amma yanzu kam hakan sai labari ta wannan namijin kokari da daraktan ke yi kawo yanzu tun zuwan sa mukamin.

By ukarofi