Daga USMAN KAROFI
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da cikakken tsaro da kulawa ga matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) a faɗin jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ƙaddamar da taron horarwa na NYSC Batch ‘C’ Stream 2 na shekarar 2024 a cibiyar horaswa ta UBEC da ke Gusau ranar Juma’a.
Da yake jawabi, Gwamna Lawal ya jinjina wa tsarin NYSC bisa rawar da yake takawa wajen haɗa kan ƙasa da samar da ƙwararrun ma’aikata a ɓangarori daban-daban. Ya ce, “A Zamfara, muna jin daɗin gudunmawar da masu yi wa ƙasa hidima ke bayarwa a ɓangarorin ilimi, lafiya da noma.” Ya kuma tabbatar da cewa dawowar zaman lafiya a jihar ya ba da damar ci gaba da gudanar da harkokin sansani cikin kwanciyar hankali.
Gwamnan ya buƙaci matasa masu yi wa ƙasa hidima su yi amfani da damar da jihar ke da ita a ɓangarorin noma da albarkatun ƙarƙashin ƙasa, tare da kira gare su da su girmama al’adu da addinan jama’ar da suke zaune tare da su. Ya kuma ƙara da cewa gwamnatinsa ta ɗauki matakan gaggawa wajen bunƙasa ɓangaren ilimi da lafiya, domin tabbatar da kyakkyawan makoma ga al’ummar jihar.
A nasa ɓangaren, Kwamandan NYSC na Jihar Zamfara, Mallam Muhammed Lawan Ahmed, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa goyon bayan da yake bai wa shirin, wanda ya tabbatar da ci gaban ayyukan NYSC a jihar. Gwamnan ya rufe taron da fatan Allah ya jagoranci masu yi wa ƙasa hidima a shekara mai amfani ga rayuwarsu da al’ummar jihar.
