Daga USMAN KAROFI
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da damar aikin gwamnati kai tsaye ga ɗalibai 16 da suka kammala karatun nas a jami’ar Sudan International University.
A ranar Alhamis, Gwamna Lawal ya gabatar da takardun shaidar kammala karatun ga ɗaliban a fadar gwamnati da ke Gusau, inda ya bayyana farin cikinsa da nasarar da suka samu duk da matsalolin da suka fuskanta a Sudan.
Sanarwar mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ta bayyana cewa ɗalibai 66 ne aka kwaso daga Sudan a shekarar 2023 saboda yaƙin da ake yi a ƙasar, ciki har da ɗalibai 16 da suka kasance a shekarar ƙarshe ta karatun nas amma ba su sami damar rubuta jarabawarsu ba kafin yaƙin ya ɓarke.
A bisa umarnin gwamnan, an tattauna da jami’ar don gudanar da jarabawarsu a Najeriya a watan Satumba 2023, inda duka suka ci jarabawarsu kuma aka basu takardun shaidar kammala karatu. Gwamnan ya yaba da hazaƙarsu tare da tabbatar musu da samun aiki kai tsaye a asibitocin jihar, domin taimakawa wajen ci gaban lafiyar jama’a.
