Hukumar Alhazan Nijeriya ta sanar da kuɗin aikin Hajjin 2025

Spread the love

Dag SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya NAHCON, ta sanar da sabon farashin kujerar aikin Hajjin bana.

A hirarsa da BBC, shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya ce kujerar aikin hajjin kamar yaushe ta kasu kashi uku inda waɗanda za su je Hajjin daga Kudancin Nijeriya kuɗinsu ya fi na waɗanda za su tashi daga Arewa maso Gabas da kuma Arewa maso yammancin Nijeriya.

Ya ce “Ga alhazan da za su tashi daga jihohin yankin arewa maso yammacin Nijeriya kamar Kano da Kaduna da Jigawa da Katsina da Zamfara da Sakkwato da Kebbi, za su biya kuɗin da ya kai naira miliyan 8.45.

“Sai kuma waɗanda za su tashi daga arewa maso gabashin Nijeriya waɗanda su sun fi kusa da Makka, wato waɗanda suka fito daga jihohin Adamawa da Yobe da Borno da Gombe da Bauchi da kuma Taraba za su biya naira miliyan 8.32.”

“Waɗanda za su tashi daga jihohin Kudancin Nijeriya kuma za su biya naira miliyan 8.78,” inji shi.

Shugaban hukumar na NAHCON, ya ce kuɗin kujerar aikin hajjin ta bana da kaɗan ya ɗara na bara.

Ya ce “Da farko mun tsorata domin muna ganin kuɗin kujerar bana zai iya kai wa naira miliyan 10 koma fiye da haka, to amma da taimakon Allah da kuma tuntuɓa da bibiyar waɗanda ke yi wa alhazai hidima a can Saudiya da muka yi shi ya sa aka samu sauƙi.”

Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya ce “Mun yi ƙoƙari mun samu sauƙi a kan kuɗaɗen da ake kashewa alhazai a Mina da wajen Arfah da Muzdalifa saboda tattaunawar da muka yi da waɗanda abin ya shafa a can.”

Shugaban hukumar alhazan na Nijeriya, ya ce a cikin wannan kuɗin kujera babu tallafin gwamnati ko kaɗan.

“Dangane da batun kuɗin guzurin alhazai kuwa a bana ma dala ɗari biyar za a bawa kowane alhaji kamar bara.”

Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya ce, sun yi gyare-gyare sosai domin gudun fuskantar matsalar da aka samu a hajjin bara musamman a zaman Mina kan batun tantunan manyan baƙi.

Kazalika ya sanar da ranar ƙarshe ta biyan kuɗin kujerar aikin hajjin bana 2025, inda ya ce “Duk maniyyacin da bai biya kuɗinsa har zuwa ranar 5 ga watan Fabrairun 2025, to gara ma ya hakura ya bari sai baɗi.

Ya ce “Akwai yarjejeniya da muka yi da mahukuntan Saudiya inda muka ajiye wa’adin biyan kuɗin don gudanar da dukkan shirye-shiryen da suka dace, to idan mutum bai biya ranar 5 ga watan Fabrairu wadda ita ce ranar ƙarshe ta biyan kuɗin, to sai dai a haɗu a hajjin badɗi na 2026.” 

By ukarofi