Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ranar Talatar da ta gabata ne aka mayar da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, Alhaji Bashir Sa’idu gidan yari da ke Kaduna.
Babbar kotun jihar ta ɗage ci gaba da sauraron buƙatar belinsa har zuwa ranar Alhamis, 23 ga watan Janairu, 2025.
An gurfanar da Sa’idu da kwamishinan kuɗi a wani lokaci a gaban babbar kotun jihar Kaduna ta biyu bisa tuhume-tuhume 10 da suka haɗa da badaƙalar kuɗi da almubazzaranci da kuma sata.
Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta da sauran laifukan da ke da alaƙa da su ta kai ƙarar kwamishinan a wata babbar kotun jihar.
Lokacin da aka gabatar da ƙarar a gaban mai shari’a Isa Aliyu a ranar Talata, an karanta tuhume-tuhume 10 a zaman wanda ake ƙara, inda ya musanta aikata laifin.
Zarge-zargen da wasu ke zargin tsohon kwamishinan ya sayar da dala miliyan 45 a cikin kuɗi mai wuya na gwamnatin jihar Kaduna kwatankwacin N18,450,000,000, a kan farashin da bai taka kara ya karya ba na N 410 kan kowace dala, maimakon daidaiton farashin kasuwa na N498 kan kowace dala , da niyyar aikata laifi, wanda ya haifar da N3,960,000,000 hasara ga gwamnati.
Mai gabatar da ƙara ya ce laifin ya faru ne a shekarar 2022, lokacin da Sa’idu ya riƙe muƙamin kwamishinan kuɗi a gwamnatin El-Rufai.
Mai gabatar da ƙara ya ci gaba da cewa Sa’idu ne ya karkatar da kuɗin N3,960,000,000, wanda ya saɓa wa sashe na 18 na dokar haramci ta ƙasa ta 2022.
