Tsofaffin janar na soji ke da hannu a haramtattun haƙar ma’adanai a Nijeriya, inji Majalisar Dattijawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Dattijawa ta yi zargin cewa wasu daga cikin jagororin sojojin da suka yi ritaya sune ke da hannu a gudanar da haramtattun haƙar ma’adanai a Nijeriya wanda hakan ke haifar da koma-baya ga faɗaɗa tattalin arziƙi a ƙasar.

Shugaban kwamitin majalisar akan harkokin cikin gida, Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana hakan a lokacin da Shugaban kwamitin ci-gaban albarkatu na majalisar, Sanata Samson Ekong yake gabatar da kasafi ga kwamitin kasaftawa.

Oshiomhole ya bayyana takaicinsa kan yadda Gwamnatin Tarayya ta gaza ɗaukar mataki a kai, ya na mai cewa lallai sai gwamnatin Shugaba Tinubu ta yaƙi ɓarnar, wanda ke yi wa tattalin arziƙin ƙasa da al’umma zagon-ƙasa.

Ya ce kamar yadda gwamnati ta ke ɗaukar matakan da suka dace wajen daƙile ayyukan ɗibar mai ba bisa doka ba a yankin Neja-delta, haka ya kamata a ce ta yi wa masu haƙar ma’adanai ta haramtattun hanyoyi.

A cewarsa, “Haƙar ma’adanai da ake yi a ƙasar, janarorin da suka yi ritaya ne suke gudanar da shi, kuma mun san su. Suna amfani da helikwaftoci wajen fitar da gwala-gwalai, inda suke samun biliyoyin daloli, yayin da ƙasar ke cikin wahala.”

Ya ƙara da cewa, a lokacin da yake shugaban jam’iyyar APC, ya rubuta wa tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari saƙo game da lamarin inda ya bayyana masa irin yadda masu bin haramtattun hanyoyin suke amfani da manyan kayan aiki wajen illata albarkatun ƙasa.

Har’ilayau, Sanata ya ce har yanzu ba a ɗauki mataki ba, ya na mai nuna tura jami’an haɗaka zuwa yankunan a matsayin abinda zai taimaka wajen magance matsalar.

By Babaji