‘Yan sanda sun fake da barazanar tsaro ne don su hana maulidi a Kano, inji Kwamishinan Labarai

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta zargi ƴan sanda da ƙoƙarin hana taron addini na ɗariƙar Tijjaniyya na shekara-shekara da ta saba yi, inda suka yi ƙaryar cewa akwai barazanar tsaro a jihar.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a Fadar Sarkin Kano a ranar Juma’ah, Kwamishinan yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya kuma musanta gargaɗin da ƴan sanda suka fitar tun da fari.

Waiya ya ce rundunar ƴan sanda kawai ta fake da barazanar tsaro ne don ta hana gudanar da taron mauludin.

Kwamishinan, wanda ya ce an kwashe kusan shekaru 40 ana gudanar da shi, ya kuma bayyana cewa duk da matakin da ƴan sanda suka ɗauka, Mauludin zai gudana kamar yadda aka tsara shi a filin wasa na Ƙofar Mata.

“Ina mai tabbatar wa waɗanda suke son halartar taron cewa gwamnatin jihar ba za ta bari a samu wata matsala ba In Shaa Allahu.”

Kazalika, ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta janye hukumomin tsaro daga wajen da aka shirya gudanar da taron yana mai cewa filin wasa na Ƙofar Mata na Jihar Kano ne.

By Babaji