Nijeriya ta tabbatar da shiga ƙungiyar ƙawancen tattalin arziƙi ta BRICS

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Nijeriya ta amince da tayin shiga ƙungiyar ƙawancen tattalin arziƙi na BRICS kamar yadda wata sanarwa da fito daga ma’aikatar harkokin ƙasashen waje ta bayyana a ranar Asabar.

ƙungiyar ta amince da Nijeriya a matsayin mamba a shekarar 2024 a yayin taronta da aka yi a ƙasar Rasha. Nijeriya ce ƙasa ta sha biyu cikin jerin sabon ƙulla ƙawancen na BRICS.

A cewar ma’aikatar harkokin ƙasashen waje, shigar Nijeriya cikin wannan ƙungiya alamu ne na irin yadda ta himmatu wajen ƙulla alaƙa da ƙasashen duniya domin inganta tattalin arziƙin ƙasa.

Ma’aikatar ta ce Nijeriya na amfani da dabarun ƙulla alaƙar ne domin cimma muradanta na samar da cigaba saboda ƙungiyar BRICS za ta bai wa ƙasashe masu tasowa damar bunƙasa kasuwanci da zuba hannun jari da sauran ƙasashe mambobin ƙungiyar.

Sai dai tsarin bai wa Nijeriya damar shiga ƙungiyar ya bambanta da na ƙasar Indonesia wacce ta shiga a ranar 7 ga watan Janairu.

Duk da cewa Nijeriya ta shiga ƙawancen, sai dai ba ta kammala zama cikakkiyar mamba saboda Nijeriya ba ta damar shiga a dama da ita wajen yanke shawarwari da suka shafi makomar ƙawancen inda cikakkun mambobi su ne ke da ikon fidda tsare-tsare da kuma cin gajiyar damarmaki da tafi da ƙungiyar.

Sai dai Nijeriya ta bayyana aniyarta ta tattaunawa da da sauran ƙasashe mambobin ƙungiyar domin a cewar ma’aikatar harkokin Nijeriya ita ce ta 9 da ta shiga ƙungiyar a matsayin ƙawa marar cikakken iko bayan ƙasashe kamar Belarus, Boliɓia, Cuba, Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda, da kuma Uzbekistan.

An kafa ƙungiyar BRICS ne a shekarar 2009 a ƙarƙashin jagorancin ƙasashen Brazil, Rasha, Indiya, da China, sai kuma ƙasar Afirka ta Kudu a shekarar 2010.

ƙungiyar dai an kafa ta ne domin yin kafaɗa da kafaɗa da ƙasashen G& da ya haɗa da bunƙasa tattalin arziƙi. Babbar manufar ƙungiyar BRICS ita ce ƙarfafa wa ƙasashen masu tasowa.

An fara amfani da kalmar “BRICS” ne a farkon shekarun 2000 domin ƙarfafa wa ƙasashe masu tasowa wajen su zama masu ƙarfin tattalin arziƙi a ƙarni na 21. tun bayan wannan lokaci ne kuma ƙungiyar take cigaba da mai da hankali wajen ƙarfafa ƙasashen masu tasowa.

A shekarar 2014, wannan ƙungiya ta ƙara faɗaɗa inda ta ƙunshi ƙasar Iran, Egypt, Ethiopia, da Tarayyar ƙasashen Larabawa.

Sannan ƙasar Saudiyya ta samu goron gayyata daga wannan ƙungiya sai dai har yanzu ba ta kai ga amince da shiga ƙungiyar ba.

By ukarofi