Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
Ganin yadda mata ke samun matsalar cutar mahaifa a lokacin da suka girma ko idan sun zo haihuwa ake wahala, gidauniyar Alhaji Ali Usman Foundation ta himmatu wajen bayar da taimakon allurar rigakafi cutar bakin mahaifa kyauta wa yara mata ‘yan shekara tara zuwa 14 a yankin ƙaramar Hukumar Toro da ke a Jihar Bauchi.
Gidauniyar ta gudanar da wannan gagarumin aiki a garin Magama Gari da ke ƙaramar Hukumar Toro jihar Bauchi cikin makon da ya wuce.
A yayin wannan aiki an wayar da kan iyaye mata kan wannan matsalar kuma sama da ‘yan mata ɗari suka karɓi allurar da kuma ilmantuwa kan matsalar cutar.
Kwamared Yusuf Aliyu Fada shugaban ƙungiyar ma’aikatan kiwon lafiya na sa kai masu bayar da agaji kyauta shine ya jagoranci gangamin allurar da wayar da kan iyaye mata don samun nasarar shirin.
Yadda cikin jawabinsa Kwamared Aliyu Fada ya bayyana cewa muhimmin abin da suke yi shine wayar da Kai da kuma bayar da allurar wacce idan za a biya a kasuwa kowace allurar ana kashe naira dubu 30.
Amma Alhaji Alli Usman ya saya kuma ya bayar don taimako a matsayinsa na ɗan ƙasa mai kishi, kuma tsohon ma’aikacin gwamnatin da ke son ganin lafiyar mutanensa ta inganta.
Malama Khadijat Abdulkadir da Malama Munirata Aliyu Jibrin na cikin ma’aikatan da suka gudanar da aikin, inda cikin jawabinsu suka yaba tare da bayyana cewa aikin ya taimaka kuma da fatar za a ci gaba da yi wa Alhaji Aliyu Usman godiya da addu’a.
Kuma ya kamata mutane su ci gaba da masa addu’a Allah ya ba shi ikon taimaka wa kan sauran cututtuka. Da fata masu hannu da shuni za su rika gudanar da irin wannan aikin don taimakon marasa ƙarfi.
Malama Habiba Magama da Hajara Yakubu da Binta da Ummi Musa da Amina wasu mata iyayen da suka bayar da yaran su don karɓar allurar rigakafin cutar bakin mahaifar, cikin jawabinsu suka godewa Alhaji Ali Usman, saboda daukar ɗawainiyar shirin allurar yadda suka gode masa tare da jan hankalin iyaye su lura da lafiyar yaransu ta hanyar zuwa asibiti a kan lokaci idan an ji matsala game da lafiya.
Malam Abdullahi Munkaila mai Unguwar Magama Gari cikin jawabinsa ya gode wa wanda suka gudanar da aikin da wanda ya ɗauki nauyin shirin. Haka kuma ya ja hankalin ‘yan siyasa da masu hannu da shuni su riƙa tallafawa masu ƙaramin ƙarfi saboda ganin yadda matsalar tattalin arziki ke sa mutane cikin wahala da kuma mutuwa saboda rashin kuɗin jinya da sayen magani.
Don haka ya yi farin ciki kuma ya gode wa wanda suka yi aikin da wanda ya bayar da dukiyarsa don taimakon matan yankin.
ɗangadiman Bauchi, Hakimin Jama’a Alhaji Bala Sulaiman a yankin Toro ya karɓi ziyarar tawagar jami’an kiwon lafiya da suka gudanar da aikin kuma ya gode wa Alhaji Ali Usman ya yi fatar ya faɗaɗa aikin taimakon zuwa fannin ilmi da tallafi kai aikin gona, saboda akwai iyaye talakawan da yaran su ke da ƙoƙari amma basu da halin taimaka musu su je manyan makarantu don haka suke zama a gida tarbiyyarsu na lalacewa.
Hakimin Jama’a Alhaji Bala Sulaiman ya ce ƙofarsa a buɗe take a duk lokacin da ake buƙatar taimakon su ko neman shawara kada a ji nauyi a same su a shirye suke wajen bayar da dukkan goyon bayan da ake buƙata.
Don haka ya buƙaci a isar da godiya ga wanda ya ɗauki nauyin shin wato Alhaji Ali Usman Foundation kuna suna masa addu’a da fatan Allah ya ba shi halin ci gaba da wannan aikin taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi.
