Al’umma su jajirce da addu’o’in fitar da ƙasa daga halin da ake ciki – Muhammad Yusuf

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Duba da yanda al’amuran rayuwa suka sauya a ƙasar nan da mutane suka tsinci kansu a yanayi da ba a taɓa tsammani ba, anyi kira ga al’umma su jajirce suyi juriya da yin addu’a Allah zai kawo mafita daga halinda ake ciki.

Manajan kamfanin sarrafa ruwan leda na Lucky dake rukunin masana’antu na Dawakin Dakata.Alhaji Muhammad Yusuf  ne ya yi  kiran da yake zantawa da yan jarida, ya yi nuni da  cewa shi shugabanci amana ce wanda yake  ya tabbatar akwai lokacin da Ubangiji zai tambaye shi amanar da ya danka masa  yakamata shugabanni suyi hattara su kiyaye  su dubi amana da Allah ya ba su, ba don sun fi wani ba, su ya zaɓa don ya jarraba su, su tsaya su dubi Allah suyi jagoranci bisa amana da adalci.

Ya ce halin da talakawa suke ciki yanzu an kai wani yanayi mai tsauri abin babu daɗi  shugabanni su dubi Allah suyi nazari akan hanyoyi da za su bi su fitar da mutane daga mawuyacin hali da suke ciki.

Da ya juya kan masana’antu ya ce yanzu abubuwa sun zama babu daɗi ana fama da matsalar wuta da tsadar kayayyakin sarrafawa, amma babban ƙalubale a gare su da suka fi fuskanta shine matsalar wuta domin daga watan Agusta na bara sai da aka nunka kuɗin wuta sau Uku daga yanda ake biya N71,50 sai da  ya koma N209 idan aka haɗa har “VAT” ma duk unit ɗaya ya kai  N226 wannnan ne halin da aka tsinci kai.

Ya ce idan kana biyan N250,000 sai ka biya  sama da N700,000 wanda ta kai a rukunin masana’antun su na Dawakin  Dakata akwai mutane da yawa   sun rufe sana’ar sun haƙura. An  yi ƙa’ida.da kamfanin rarraba wutar za a riƙa bada wutar a “Ban A” saboda sun raba abin kashi kashi ne, akwai ban A da B da C.Idan kana ban A zaka sami wuta na awa 20 a wuni, amma takan  kai   wata rana ma ba zaka sami wutar awa Takwas ba.Har ta kai a mako suna a “Ban A “amma basa samun wuta ta kwana Uku amma za a kawo musu Bill a kuɗin  ban A.

Ya yi nuni da cewa ba yanda za suyi domin sun yi ƙorafe ƙorafe ga waɗanda abin yake hannunsu  amma ba wani sauyi wannan na daga manyan ƙalubale da masana’antu ke fuskanta  haka a ɓangaren kayan aiki shi kansa ya na tsada ,musamman su masu yin ruwan  leda da ake saye a baya Naira miliyan ɗaya yanzu sai ka sa sama da da Miliyan Uku haka ake tafiya harkokin babu daɗi ana yi yafi ace ba ayi.

Alhaji Muhammad Yusuf Manajan  kamfanin sarrafa  ruwan leda na Lucky ya ce wannan tasa abubuwa suke  raguwa, hatta a ma’aikata  domin ba zaka iya ɗaukar masu yawa ba duk  abubuwa da kake iya yi  a baya yanzu ba zai yiwu ba, ko yanayi na buƙatun da za ace yau anyi kaza anyi kaza ko motar ka ta tsufa da take kai maka kaya ka sayar da ita ka ƙara kuɗi ka sayi sabuwa ya gagara, yanzu gidan ruwa ba kowanne bane ya isa ya cire kuɗi a lokaci ɗaya ya je ya sayo motar ɗaukar kaya sai dai wacce kake da ita ka lallaɓa ta.

By ukarofi