
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ofishin Hukumar Sufurin Jiragen sama na Al’umma (NCAA) ta dakatar da Kamfanin jiragen sama na Max Air daga gudanar da harkokinsa biyo bayan tsallake rijiya da baya da ɗaya daga cikin jiragensa ya yi a Kano.
Jirgin, ƙirar B734 mai lamba 5N-MBD, an samu ɗaya daga cikin tayoyinsa ya fashe ne a lokacin da ya nufi sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a ranar Talata da misalin ƙarfe 10:51 na dare.
Wannan shi ne al’amari na uku cikin watanni 3 da makamancin haka yake faruwa da jiragen kamfanin.
Duk da cewa an fitar da fasinjoji 53 cikin ƙoshin lafiya daga cikin jirgin, Hukumar kula da Tashoshin Jiragen sama ta Ƙasa (FAAN) ta sake buɗe hanyar tashi sama na filin da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Laraba.
Tuni dai Cibiyar Bincike ta bada Kariya ta Ƙasa (NSIB) ta fara bincike game da lamarin, inda NCAA a wata sanarwa ta ce za ta bada duk wani taimako da ake buƙata, wanda sai bayan fitar da rahoton ne, za a bada cikakken bayani game da musabbabin faruwar al’amarin.
Daraktan yaɗa labaran NCAA, Michael Achimugu a sanarwar, ya ce an fara gudanar da bincike kan Max Air da jami’an gudanarwa.
Ya ce a yayin haka ne aka dakatar da jiragen kamfanin na gida daga zirga-zirga har na tsawon watanni uku daga ranar 31 ga watan Junairu.
Ya ƙara da cewa, kamfanin zai dawo aiki ne a lokacin da hukumar ta kammala bincike game da lamarin.
