



Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya yaba wa Hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS bayan kama wani wajen ajiyar makamai a jihar.
A ranar Talata ne daraktan DSS na jihar ya haska makamai da alburusan da aka gano ga Gwamna Lawal a Fadar Gwamnatin jihar dake Gusau.
Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa, makaman da aka ƙwace sun haɗa da gurnet na RPG, bindigogin ‘machine gun’ guda biyu, Ak47 guda 9, ƙananun bindiga 2, mujallu 9 da kuma alburusai sama da guda dubu.
Sanarwar ta kuma ce jami’an DSS sun bi diddigin ɗan bindigar da ake zargi tun daga Jamhuriyar Nijar, inda aka kama shi akan babban titin Zurmi/ Ƙauran Namoda a jihar.
A lokacin da ya ke ganin makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya jinjina wa haɗakar dakarun tsaro tsakanin sojoji da ƴan sanda musamman DSS wajen daƙile ta’addanci a jihar.
Ya ce nasarori a ƙoƙarin magance ta’addanci a jihar sun samu ne ta hanyoyin haɗin-gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da gudunmawar da gwamnatin jihar take bai wa harkar tsaro.
Ya kuma ce za su cigaba da tallafa wa jami’ai ta hanyoyin da suka dace wajen ɗorewa da ƙarfafa musu akan ayyukansu.
Har’ilayau Gwamna Lawal ya ce abu ne da zai ɗauki hankalin al’umma cewa mafiya yawancin ɓarayin da aka kama ƴan Zamfara ne ba ƴan waje ba, ya na mai cewa an kama da dama daga cikin su a makonnin da suka gabata.
“Ta’addanci yana durƙushewa a Zamfara. Mun ga haka. Ina kira ga al’ummar Zamfara da su bada dukkan taimakon da ake buƙata ga jami’ai”, inji gwamnan.
