INEC ba ta ƙarbar tallafi kai tsaye daga masu bayarwa

Spread the love

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba ta karɓar kuɗi kai tsaye daga ƙungiyoyin bada tallafi, kamar yadda wasu ke zato. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan yayin da sabon jakadan Tarayyar Turai (EU) a Najeriya, Ambasada Gautier Mignot, ya kai ziyarar ban girma hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Yakubu ya ce, duk da cewa Tarayyar Turai da wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na ba da gudunmawa wajen inganta tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya, INEC ba ta da wani asusu da ke ajiye kuɗaɗen tallafi daga waɗannan ƙungiyoyi. Ya bayyana cewa tallafin da ake samu na zuwa ne ta hanyar bayar da kayan aiki, horarwa, da tallafin fasaha daga abokan hulɗar hukumar.

A nasa ɓangaren, Ambasada Mignot ya jaddada cewa Tarayyar Turai na goyon bayan ci gaban dimokuraɗiyya a Najeriya ta hanyoyi daban-daban, ba wai ta hanyar kuɗi kawai ba. Ya ce EU na bibiyar harkokin zaɓe a matakan jiha da tarayya domin ganin an inganta tsarin gudanar da zaɓe.

Shugaban INEC ya kuma bayyana cewa tun bayan kammala zaɓen 2023, hukumar ta samu shawarwari da rahotanni daga ƙungiyoyin sa ido 206 da aka tantance domin bin diddigin zaɓe. Ya ce INEC ta fara aiwatar da wasu shawarwarin da aka bayar domin inganta tsarin zaɓe, ciki har da horar da ma’aikatan zaɓe da amfani da sabbin fasahohi wajen tantance masu kaɗa ƙuri’a ’a.

A ƙarshe, Yakubu ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da aiki tare da abokan huldarta domin inganta sahihancin zaɓe a Najeriya. Ya ce INEC tana ƙoƙarin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe mai inganci da adalci, inda ya jaddada cewa gwamnati ce ke da alhakin samar da kuɗaɗen gudanar da manyan ayyukan zaɓe, kamar yin rijistar masu kaɗa ƙuri’’a da samar da katunan zaɓe (PVC).

By ukarofi