Tankar mai ta ƙara fashewa a Jigawa

Spread the love

Wata mummunar gobara ta tashi a tashar saida mai da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa, a daren Alhamis. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare a Shakkotu, kan titin Kiyawa, bayan da wata motar dakon fetur ta fashe yayin da ake sauke mai a gidan mai.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta haifar da tashin hankali, inda jama’a suka rika gudu don ceton rayukansu. Wani shaidar gani da ido, Baba Nura, ya bayyana cewa ya ji ƙarar fashewa, kuma da ya isa wurin, sai ya ga gobara ta mamaye yankin. An ruwaito cewa gidan man da wasu kadarori da ke kusa sun lalace sakamakon wutar.

Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar Jigawa, SP Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun sami rahoton gobarar da misalin 8:00 na dare. Ya ce jami’an tsaro da ‘yan kwana-kwana sun garzaya wurin domin shawo kan lamarin. Ya kuma ƙara da cewa, har zuwa yanzu ba a samu rahoton mutuwa ba, sai dai ana ci gaba da bincike kan ɓarnar da gobarar ta haifar.

By ukarofi