aga USMAN KAROFI
Tsohon Shugaban mulkin soja kuma mai jagorantar kwamitin zaman lafiya na Ƙasa (NPC), Janar Abdulsalami Abubakar (ritaya), ya bayyana cewa babu madadin dimokuraɗiyya a Najeriya, yana mai buƙatar ‘yan ƙasa su ci gaba da inganta tsarin mulkin na jama’a. Ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da wani littafi da majalisar jam’iyyun siyasa (IPAC) ta wallafa, mai taken “Shekaru 100 na Ci gaban jam’iyyun siyasa a Najeriya – Bukatar tsaro da kwanciyar hankali a Siyasa.”
A nasa ɓangaren, shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su bi doka da ƙa’idojin zaɓe domin tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin dimokuraɗiyya. Ya bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin INEC da IPAC na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ingantaccen tsarin zaɓe, da ƙarfafa bin dokoki da ƙa’idojin jam’iyyun siyasa.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim, ya jaddada buƙatar tattaunawa a ƙasa domin magance rashin amincewa da juna da ke tsakanin ƙabilu da yankunan Najeriya. Ya ce matsalolin da ake fuskanta tun daga haɗewar ƙasar a 1914 har zuwa yanzu sun samo asali ne daga rashin fahimtar juna, wanda ke kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Duk da waɗannan ƙalubale, masana harkokin siyasa sun yi ittifaki kan cewa dimokuraɗiyya ita ce hanya mafi inganci ta tafiyar da mulki a Najeriya. Sun buƙaci a ƙara mai da hankali kan gyaran dokokin zaɓe, ƙarfafa tsare-tsaren jam’iyyun siyasa, da tabbatar da cewa zaɓen shugabanni yana wakiltar muradin jama’a.
