A yau Shugaba Bola Tinubu ya yi sallar Juma’a da Khalifa Sheikh Mahi Ibrahim Inyass a masallacin Fadar Shugaban Ƙasa. Khalifan ya yi wa Nijeriya addu’ar zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa, kana ya yi wa Shugaban Ƙasar fatan samin nasarar ayyukan da ya ke yi na sake raya ƙasa.



