Ci gaba da zama Sufeto Janar da Egbetokun ke yi bai saɓa doka ba duk da cika shekarun ritaya – Ministan Shari’a

Spread the love

Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa cigaban zama Sufeto Janar na ‘yan sanda da Kayode Egbetokun ke yi, ya yi daidai da doka.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, Fagbemi ya bayyana cewa naɗin Egbetokun da ya fara aiki tun ranar 31 ga Oktoba, 2023, zai kare ne a ranar 4 ga Satumba, 2024, lokacin da zai cika shekaru 60 da haihuwa.

“Koyaya, kafin shekarun ritayarsa su cika, an yi gyara ga dokar ‘yan sanda wanda ya baiwa mai riƙe da wannan muƙami damar kammala wa’adin shekaru huɗu da aka tanada a ƙarƙashin Sashe na 7 (6) na dokar, duk da cewa ya kai shekaru 60.”

Ya ƙara da cewa, gyaran dokar da aka yi a shekarar 2024 ya tabbatar da cewa wa’adin Egbetokun zai ƙare ne a ranar 31 ga Oktoba, 2027, domin cika cikakken wa’adin shekaru huɗu da aka bashi.

“Don kauce wa ruɗani, ci gaba da zamansa a ofis ya yi daidai da tanadin sabuwar dokar da aka yi wa kwaskwarima, wacce ta baiwa mai riƙe da muƙamin wa’adin shekaru huɗu daga ranar da aka naɗa shi a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sanda.”

Ministan ya ce wannan bayani na da muhimmanci domin wayar da kan al’umma game da halaccin cigaban wa’adin Egbetokun a ofis.

By ukarofi