
Daga BELLO A. BABAJI
Darakta-Janar na Hukumar kula da ɗaliban da ke yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Yusha’u Ahmed ya sanar da cewa a watan Fabrairu, 2025 ne ƴan hidimar ƙasa za su fara karɓar alawus ɗin N77,000 a madadin N33,000 da aka saba biyan su.
A ranar Alhamis ne Daraktan ya bayyana hakan a Katsina, a lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga ƴan zangon ‘C’ 2024, ɗiba na biyu.
Ya ce an sanya karin kuɗaɗen ne a kasafin kuɗin 2025 na Gwamnatin Tarayya waɗanda za a fara biya da zarar an tabbatar da shi.
Ya kuma jaddada ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na cigaba da kula da masu yi wa ƙasa hidima, ya na mai kira a gare su da su tsare ayyukansu bisa gaskiya da adalci.
Ya ƙara da cewa, ba za a tura kowane ɗan NYSC yin hidima a wuraren da suke da barazanar tsaro ba saboda tabbatar da kula ga rayukansu da lafiyarsu.
