
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jami’yyar PDP, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da ƙarfin mulki wajen ƙaddamar da yaƙi kan ƴan ɓangaren adawa.
A wani saƙo da aka wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya yi alla-wadai da kama Farfesa Usman Yusuf, mai sharhi akan al’amuran yau da kullum, ya na mai cewa an siyaysantar da kama shi duk da cewa akwai zargi akansa da ya samo asali daga gwamnatin da ta gabata.
Ya ce gwamantin Tinubu tana tafiya ne da waɗanda akwai zarge-zarge akansu daga hukumomin cikin gida da na Ƙasa-da-ƙasa.
Ya kuma soki Gwamnatin da zargin yin amfani da yaranta wajen gudanar da binciken da saɓa wa ƙa’idojin hukumomi wajen tsangwamar waɗanda ba ruwansu.
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa, a kullum ayyukan gwamnatin Tinubu tana nuna wa al’umma ƙarara cewa ba yaƙi take da rashawa ba, a madadin haka sai ta riƙa ƙoƙarin daƙile tsarin ƴan adawa.
Hakan na zuwa ne a lokacin da al’umma ke nuna damuwa bisa zargin gwamnati da nuna muzgunawa ga ƴan adawa.
A wata Junairun 2024 ne hukumar ƴan sanda ta gayyaci Omoyele Sowore, wanda shi ya jagoranci ‘Revolutionnow Movement’ inda Ofishin Binciken manyan laifuka ya gudanar da bincike akan sa.
Baya ga haka ne ƴan sandan suka bada belinsa, amma kasancewar bai cika ƙa’idar belin ba, sai aka ajiye shi, inda daga baya aka maka shi a kotun bisa tuhumar laifuka 16 masu alaƙa da yanar gizo. A nan kuma aka yanke masa hukuncin biyan Naira miliyan 10 da mutum ɗaya da zai tsaya masa.
Mutum na biyu ne shine Farfesa Usman Yusuf, tsohon babban sakataren Hukumar NHIS da EFCC ta kama a ranar Laraba bisa laifin almundahana, kamar yadda Kakakinta, Dele Oyewale ya bayyana.
