Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 60, sun kama 50 a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya cikin makonni uku.
Wasu ‘yan bindiga sun kashe kusan sojojin Nijeriya 20 a ranar Juma’a bayan sun kai musu farmaki a sansanin sojoji da ke Mallam Fatori (wani gari tsakanin Nijeriya da Nijar) a jihar Borno.
A cikin waɗanda aka kashe har da laftanar kanar wanda shi ne kwamandan rukunin sojojin kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reauters ya rawaito.
Rahotanni sun ce jami’an sojin Nijeriya da dama sun samu rauni a lokacin harin da har yanzu ba dan su waye da alhakin kai shi ba.
Boko Haram da sauran tsaginta na ISWAP, yawanci su ne suka fi gudanar da ayyukansu na ta’addanci a Borno duk da ISWAP ta fi yawan iƙirarin kai hare-haren. Sai dai har zuwa yanzu ba ta fito ta ce komai ba kan harin.
Boko Haram a yanzu ta daina sakin komai ta intanet tun bayan kashe mata ƙwararren ɗan soshiyal midiya ɗinta da aka yi a shekarun baya.
Mutanen garin da wasu jami’an tsaro sun bayyana wa Reuters cewa maharan sun zo ne a motoci Masu ɗauke da bindigu tare da farmakar sansanin sojojin Nijeriya bataliya ta 249 da ke Malam-Fatori. Da isowarsu suka buɗe wuta a kan mutanen gari da jami’an sojin.
Wata majiya, wacce ba a ba ta izinin magana ba a hukumance ta labarta cewa, an kashe sojojin Nijeriya 20 a yayin da suke ƙoƙarin fatattakar ‘yan bindigar wanda suka shafe awanni uku suna yi.
Jami’an tsaron dai ba su fitar da wata sanarwar a hukumance ba. Kuma mai magana da yawun rundunar, Onyenma Nwachuckwu, bai ce komai ba duk da sakon kar ta kwana da muka aike masa domin neman ƙarin haske kan lamarin.
Sai dai wani ɗan sa kai da ke taimaka wa rundunar sojin Nijeriya, ya ce, maharan sun ƙone wasu gidaje wanda ya tilasta wa mutane guduwa daga yankin.
“Sun yi ƙoƙarin wayar da kan mazauna yankin,” a cewar Reuters.
Wannan abu ya faru ne a kan iyakar Nijeriya da Nijar inda Lakurawa suka fi ƙarfi kuma a kan same su a kan iyakokin ƙasahen biyu a yankin Arewa maso yamma na Nijeriya.
A baya dai an alaƙanta ta da ƙungiyar al-ƙaeda. Sai dai masu bincike sun ce suna da alaƙa ne da rundunar ISGS mai ayyukan ta’addancin a yankin Sahel.
Dukkan waɗannan ƙungiyoyi suna ayyukan ta’addancin tare da biyayya ga ƙungiyar ta’addanci ta Islamic state.
Sai dai ISGS na gudanar da ayyukanta ne ƙasashen da ke yankin Sahel inda and ISWAP ke ayyukanta a yankin kogin Chadi da ya haɗa ƙasashe kamar Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.
Dukkan ƙungiyoyin dai na kai wa al’umma da jami’an tsaro ne hare-hare.
