Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Jagoran siyasar ƙaramar Hukumar Nasarawa a Jam’iyyar NNPP, Alhaji Garba Mustapha Mai Sikeli, ya bayyana cewa ilimi da Allah ya bai wa shugaban hukumar makarantun kimiyya da fasaha ta Kano, wato STSB da kuma muƙamin da Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ba shi na makarantun sakandaren kimiyya da fasaha na jihar da taimakon da yake yi wa al’umma da wanda ya sani da wanda bai sani ba daga ko’ina ya ke matuƙar ya cancanci taimako da buƙatar hakan, Farfesa ɗahiru Sale Muhammad na taimaka masa kuma wannan ne dalilin da al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa musamman mabiya Kwankwasiyya da gwamnatin Kano da kuma jagoran siyasar Kano Sanata Rabiu Musa kwankwaso al’ummar Nasarawa ta ga yada ce su karrama Farfesa ɗahiru da lambar girmamawa a madadin al’ummar Nasarawa masu ra’ayin cigaban al’ummar Jihar Kano da ma Nijeriya bakiɗaya, kamar dai yadda ya bayyana a ranar Lahadi da ta gabata a hedkwatar jam’iyyar NNPP da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano.
Haka kuma ya yaba masa kan yadda ya kawo cigaba da amanar da gwamnan Jihar Kano ya ba shi da kuma yadda ya rungumi al’umma ba tare da nuna bambanci ko raina mutane ba, wanda a cewarsa wannan ita ce babbar aƙidar gwamnatin Kwankwasiyya a ko’ina.
Ya kuma buƙaci ɗaukacin masu muƙamai a wannan gwamnati da sauran al’umma da mawadata da su yi koyi da Farfesa ɗahiru Sale Muhammad.
A nasa jawabin babban baƙo Hon. Yusuf Imam Ogan ɓoye, shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, ya ce suna da ruwa da tsaki kuma su ne kan gaba wajen ganin an karrama Farfesa ɗahiru musamman yadda yake taimakawa wajen ganin duk waɗanda suka cancanci shiga makarantun hukumar STSB sun samu gurbi, domin dai faɗaɗa ilimin kimiyya da fasaha a tsakanin matasa.
Shi ma Alhaji Aminu Maifamfo DMD, wani mai taimakawa al’umma ta fuskar ilimi da sauransu, ya bayyana farin cikinsa da yadda wasu ƙungiyoyi da al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa suka ga ya dace su karrama ɗansu kan irin gudummawar da yake bayarwa a koda aushe.
A ƙarshe shugaban hukumar STSB ya bayyana godiyarsa ga mahaliccinmu da godiyarsa ga Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabiru Yusuf, da mataimakinsa Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo, da jagoran Kwankwasiyya da kuma ɗaukacin al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa, musamman ‘yan Kwankwasiyya da suka ga ya dace su karrama shi a matsayin ƙarfafa gwiwa don cigaba da yi wa al’umma hidima domin cigabansu.
Hakazalika ya yaba wa ɗaukacin daraktocin hukumar STSB da ɗaukacin ma’aikatan wannan hukuma da ma duk wanda ya taimaka wajen ganin an samu nasara a wannan taro dama wannan hukuma da al’ummar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.
Taron dai ya samu halartar ɗimbin jama’a, inda manyan baƙi da dama suka gabatar da jawabansu kan gamsuwa da halayen Farfesa ɗahiru.
