Da Ɗumi-Ɗumi: Matatar Ɗangote ta rage farashin mai zuwa N890 duk lita

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Matatar man Ɗangote ta rage farashin man fetur daga N950 zuwa N890 a duk lita, farawa daga ranar Asabar. Kamfanin ya bayyana cewa wannan mataki na da nasaba da sauyin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya, wanda ke nuna raguwar tsadar kayayyakin makamashi.

A cikin wata sanarwa da Anthony Chiejina, babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin ya fitar, matatar ta ce, rage farashin zai kawo sauƙi ga ‘yan Najeriya, tare da rage yawan farashin kayayyaki da na sufuri. Kamfanin ya kuma buƙaci dillalan mai su tabbatar da cewa wannan ragi ya isa ga al’umma yadda ya kamata.

Matatar ta jaddada goyon bayanta ga ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da wadatar Najeriya da kayan man fetur. Kamfanin ya ce rage farashin zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, tare da ƙara wa Najeriya ƙaimi a matsayin jagaba a fitar da kayayyakin man fetur zuwa ƙasashen waje.

By ukarofi