
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya ta bayyana kama Farfesa Usman Yusuf da Hukumar EFCC ta yi a matsayin siyasa don hana tasirin masu ƙalubalantar matakan gwamnati da ke matsa wa al’umma.
A ranar 29 ga wata Junairu ne EFCC ta kama farfesan, wanda aka gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja.
Alƙali Chinyere E Nwecheonwu, wadda ita ke sauraron ƙarar da aka shigar akansa, ta ɗage zama a kai zuwa ranar 3 ga watan Fabrairu.
A wata sanarwa da Kakakinta, Farfesa Abubakar Jika Jiddere ya fitar, ƙungiyar ta yi kira da a sako Farfesa Yusuf, ta na mai cewa hakan amfani ne da ƙarfin mulki wajen hana ƴan adawa su bayyana ra’ayoyinsu a madadin al’umma.
Ya kuma ce ana sane tare da shirya hana ƴan tsagin adawa muryar faɗa a-ji da kuma dawo da ƴancin demokraɗiyya da ƴan Nijeriya suka samu nasara a kai tsawon lokaci wajen yaƙi da azzalumar gwamnati da dukkanin nau’ukan matsi na rashin tausayi.
