Daga IBRAHIM MUHAMMAD
Ambasada Dakta Bashir Yusuf Abdullahi, Mataimakin Shugaban ƙungiyar Kasuwar Kwanar Singa da aka fi sani da ‘SIMDA’, ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu Allah na kawo sauƙi na farashin kayan masarufi yana raguwa duba da duk shekara akwai yanayi ake samu, wannan shekara Allah ya kawo sauƙi tun daga yanzu akan kayan amfanin yau da kullum na al’umma.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ’yan jarida ya ce su kansu yan kasuwa suna kuka da cewa kaya ba sa sayuwa sai ma faɗuwa da suke saboda tsada, sannan wani lokacin ma irin wannan na gabatowar azumin watan Ramadan sai a ga kaya suna ta tashi, kuma ba domin son yan kasuwar ba yanayi ne amma a wannan karo duk wanda ka tambaya a kasuwa da daɗi babu daɗi zai gaya maka farashin kaya na sauka ba kamar a baya ba.
Ambasada Bashir Abdullahi ya ce fatan da suke da yardar Allah nan da cikin watan Azumi kayayyaki zasu ci gaba da sauka al’umma su sami sauƙin yin azumi a gama lafiya.
Ya yi kira akan yan kasuwa manya da ƙanana akan kowa ya ji tsoron Allah idan akace kaya ya sauka ka samo cikin rangwame yakamata ka yi duba akan abinda ka sayo da yanda za ka sayar, domin Allah yana ganin ka, idan ka bar shi a tsada baka san lokacinda asara za ta zo maka ba, duk waɗansu asara da za a ga yazo akwai dalilinsa, wani ko da Allah ya ƙaddara ɗin zaka ga wani abu akwai sababi na wani yayi wani abu yana ganin wayon sane ko dabarar sa, sai Ubangiji ya nuna masa ta wani ɓangare, amma idan aka ji tsoron Allah aka duba aka tausaya sai kaga Allah ya tausaya ko asarar ce ta zo sai tazo mai sauƙi.
Ambasa Bashir Yusuf Abdullahi ya ce al’amarin harkar Dala da ake amfani dashi wajen kasuwanci abin ya taɓarɓare daga sama ne, duba da a shekarun baya za a ga farashin a ƙasa ne, amma yanzu za kaji anyi Kasafi akan wani mataki na Dala duk iya ƙoƙarinka baka isa kayi ƙasa da wannan matsayin na sama da aka yi ba, dole sai dai ka bi,alhakin Gwamnati ne ta samar da daidaito a farashin Dala hakan zai taimaka.
