
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince ta ware kuɗaɗen ne a yayin zaman Majalisar Zartarwa a jiya Litinin 3 ga watan Fabrairu, a Fadar S
hugaban ƙasa.
Haka kuma, FEC ta amince da kasa aikin hanyar zuwa matakai biyu don samar da ingantaccen aiki akan lokaci.
A yayin ganawa da manema labarai bayan kammala taron, Ministan ayyuka, David Umahi ya bayyana cewa sashe na farko zai tashi daga kan iyakar Babban Birnin Tarayya Abuja zuwa Jihar Neja, wanda aka ƙara wa kilomita 5.71 kan ainihin taswirar aikin na farko, inda sashe na biyu ya samu ƙarin yankuna acikin Jihar Kano, wanda ke da tsawon kilomita 17.
Umahi ya ce yayin gudanar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa masu zuwa, irin manyan titin Lokoja-Benin da Abuja-Kano, za su yi amfani da ingantattun kwalta maimakon wanda aka saba gani a kullum da ke saurin fashewa.
Ministan ya ƙara da cewa, “a wannan karon ba za mu lamunci jan-ƙafa ko wani uziri irin na yin amfani da kayan aikin da zafin rana ka iya yi wa lahani ba, maimakon haka za mu gyara wuraren da suka lalace a baya kana mu tsaurara sanya ido sosai akan aikin.”
Gwamatin ta kuma amince da ware wani kasafin na Naira biliyan 18 don sake gina hanyar Wusasa zuwa Jos dake Jihar Kaduna.
