Jihar Sokoto ta bayyana shirin kawar da cututtukan yankin da aka mance dasu (NTDs) baki ɗaya, kamar yadda Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Faruk Umar Abubakar, ya sanar a bikin ranar duniya ta NTDs ta 2025. Taron, wanda ma’aikatar lafiya ta jihar ta shirya tare da haɗin gwiwar Sight Savers, ya nuna irin ci gaban da aka samu a yaƙin da ake da waɗannan cututtuka.
Dr. Abubakar ya bayyana cewa har yanzu akwai manyan cututtuka biyar da jihar ke fuskanta, ciki har da trachoma, onchocerciasis, lymphatic filariasis, schistosomiasis, da cututtukan ƙwayoyin tsutsotsi da ke shiga ta cikin ƙasa. Ya ce an samu gagarumin ci gaba, musamman wajen rage yawan garuruwan da ke fama da trachoma daga 14 zuwa sifili, abin da ke nuna raguwar cutar a jihar.
A yayin taron, Shugaban Shirin NTDs na jihar, Suleiman Mohammed Wamakko, ya ja hankalin jama’a kan muhimmancin tsaftar jiki da muhalli. Haka nan wasu manyan jami’an lafiya da wakilan ƙungiyoyin ci gaba sun tofa albarkacin bakinsu, suna jaddada muhimmancin haɗin gwiwa wajen kawar da cututtukan a jihar Sokoto.
