



Daga BELLO A. BABAJI
Kwamandan Kwalejin Koyon Yaƙi ta Sojoji (AWCN), Manjo-Janar Umar Mohammed Alƙali, ya karrama wasu manyan jami’an makarantar da kyautar ‘Distinguished Fellow Award’ kan ƙoƙarinsu ga ilimin sojoji da samar da ci-gaba a jagoranci na gari.
A ranar 3 ga watan Fabrairu ne aka gudanar da bikin bada lambar girmamawar ga jami’an masu muƙamin Birgediya Janar, waɗanda suka haɗa da AM Dikko (Daraktan Yaƙi da Tsare-tsare) da AU Abdul (Daraktan Shirye-shirye) da kuma NE Okoloagu (Daraktan Nazarin Sojoji da Alaƙar hukumomi).
Hakan ya samu ne bayan nuna sadaukarwa da jami’an suka yi a bakin ayyukansu, wadda ta kai ga nasarar ci-gaba a makarantar.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na kwalejin, Hashimu Sa’ad Abdullahi ya fitar, Manjo-Janar Alƙali ya yaba wa sojojin ganin yadda suka taimaka da nuna jajircewarsu ga ci-gaban kwalejin, ya na mai kira a gare su da ɗore akan haka.
Manyan jami’an sojoji ne suka halarci taron da wasu mambobin ma’aikatan kwalejin.
