
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya jagoranci wasu manyan jami’an gwamnati zuwa gidan iyalan marigayi Sanata Isah Kachako, wanda ya rasu kwanaki uku da suka gabata bayan fama da wani dogon rashin lafiya.
Cikin wata takarda da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, a ranar Talata, Gwamna Abba ya bayyana mutuwar Sanatan a matsayin babban rashi ga al’ummar Kano da ma ƙasa baki ɗaya sakamakon gudunmawarsa ga ci-gaban ƙasa.
Ya ce mutum ne wanda ya kasance mai sadaukarwa a matsayinsa na tsohon malamin makaranta, jami’in soja, kuma gogaggen ɗan siyasa, wanda ya tsaya wajen inganta al’umma.
A madadinsa da sauran al’ummar jihar, gwamnan ya yi masa fatan samun rahamar Allah da kuma haƙurin juriya ga iyalan da ya bari.
Sanata Isah ya taɓa zama gwamnan Jihar Katsina na riƙon ƙwarya da kuma mai taimaka wa marigayi tsohon shugaban mulkin Soja, Janar Sani Abacha.
Haka kuma ya na ɗaya daga cikin waɗanda suka samar da jam’iyyar APC da kuma riƙe muƙamin Turkin Kachako.
Kazalika, ya rayu da mata uku, ƴaƴa bakwai da jikoki da dama. Daga cikin ƴaƴan akwai jami’in Hukumar Kula da Ci-gaban Arewa maso Gabas, Yusuf Isah Kachako.
