
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya tabbatar da ɓarakar da ke tsakanin sa da magajinsa, Gwamna Uba Sani, ya na mai alaƙanta shirin tura kuɗi (conditional cash transfer) na Shugaba Bola Tinubu a matsayin abin da ya shiga tsakaninsu.
Hakan na zuwa ne a lokacin da Gwamna Uba Sani ya musanta duk wani rikici da ke tsakaninsu a yayin wata hira ta gidan telebijin na TVC a ranar Litinin, inda ya haƙiƙance akan cewa alaƙarsu tana nan yadda take a baya.
Gwamnan ya kuma yi tsokaci ga ƴan siyasar da ke ƙoƙarin yin nasara akan Shugaba Tinubu a zaɓen 2027, a inda ya bayyana su a matsayin masu kwaɗayin mulki, waɗanda suka gaza yin nasara a wasu oifsoshi da suka riƙe.
Ya ce irinsu na ƙoƙarin haɗewa don dawo wa mulki, ya na mai cewa mafi yawancinsu suna cikin gwamnati shekaru biyu da suka gabata, amma babu abinda suka taɓuka.
Ya kuma ce a tarihin Nijeriya, babu wani shugaba da ya yi ƙoƙarin bin tsarin demokraɗiyya kamar yadda Shugaba Tinubu ya ke yi a yanzu.
Saidai, kamar yadda ya wallafa a shafin X, El-Rufa’i ya yi watsi da kalaman gwamnan inda ya zargi biyayyarsa ga Shugaba Tinubu ta samu ne sakamakon bai wa Kaduna Naira biliyan 150 da Gwamnatin Tarayya ta yi na raba wa al’umma a tsawon watanni 18.
Ya kuma bayyana gwamnan a matsayin wanda ke tozarta Kaduna inda ya ce duk da cewa an samun kuɗaɗen, al’umma ne kaɗai za su yi hukunci, ya na mai ƙalubalantarsa da ya kare Tinubu a idon ƴan jihar.
Lamarin siyasar jagororin biyu ya fara ɗaukar ɗumi ne a lokacin da Majalisar Dokokin jihar ta zargi gwamnatin El-Rufa’i da sauya aƙalar Naira biliyan 432 wanda hakan ya jefa jihar cikin matsanancin bashi.
