Da Ɗumi-Ɗumi: Hukumar Alhazan Sokoto ta nemi NAHCON ta ƙara wa’adin rajista ga mahajjatan 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yayin da ake cigaba da shirye-shiryen zuwa aikin hajjin shekarar 2025, maniyyata 1,700 ne daga jihar Sokoto suka biya kuɗi a karon farko.

Hukumar Jigilar Alhazan jihar ta samu masauki da shirya bada kula ga mahajjatan a ƙasa mai tsarki.

Kawo yanzu kimanin Naira biliyan 5 ne jihar ta aika wa Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON).

A wata sanarwa da Babban jami’in yaɗa labaran hukumar, Faruku Umar ya fitar, Sakataren hukumar, Ladan Ibrahim ya koka kan yadda da dama daga maniyyata musamma mazauna kauyuka ba su kammala biyan kuɗaɗensu ba.

Ya yi kira ga NAHCON da ta ƙara wa’adin sati biyu don don ba su damar kammalawa.

Ya kuma ce a baya akan ba su damar biya har zuwa bayan watan Ramadana, ya na mai cewa ƙara wa’adin zai taimaka wajen tabbatar da cike guraben da aka ba su na mahajjatan.

Haka kuma sanarwar ta ce hukumar ta na tattaunawa da Gwamnatin jihar don samun agaji na kuɗi da zai taimaka wa mahajjatan.

Ya ƙara da cewa hukumar na cigaba da aiki tuƙuru wajen ganin an gudanar da harkokin hajji cikin lumana ga dukkan alhazan.

By Babaji