Daga USMAN KAROFI
Bayan korar Ohinoyin Ebiraland, Mai Martaba Mohammed Ahmed Tijani Anaje, da wata babbar kotu a Lokoja ta yi, gwamnatin jihar Kogi ta bayyana aniyarta na ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.
Kwamishinan Shari’a na jihar Kogi, Muiz Abdullahi, ya bayyana hakan a ranar Litinin a Lokoja, yana mai cewa Gwamna Ahmed Usman Ododo ya umarce shi da ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun. Ya ce gwamnati na da ƙwarin gwiwa cewa za a samu sauyin hukuncin, don haka ya buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu su guji duk wani abu da ka iya saɓa wa doka.
Kotun jihar ta yanke hukunci ne bayan ƙarar da wasu mutane uku suka shigar, inda suka ƙalubalanci naɗin Ohinoyin da tsohon gwamna Yahaya Bello ya yi. Mai shari’a Umar Salisu ya umarci Tijani Ahmed-Anaje da ya daina nuna kansa a matsayin Ohinoyin Ebiraland, tare da bayar da umarnin sake gudanar da sabon zaɓen sabon sarki bisa ƙa’ida.
