Daga USMAN KAROFI
Mataimakin shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya buƙaci dukkan ‘yan ƙasa da su haɗa hannu don inganta tattalin arzikin Najeriya, tare da bayyana goyon bayansa ga shirin “Naija Creates” . Ya ce wannan shiri, wanda Mo Abudu, Shugabar Ebony Life Group, ke jagoranta, yana da damar zama babban shirin diflomasiyyar al’adu na Najeriya wanda zai bunƙasa ƙasar ta fuskar yawon buɗe ido, kiɗa, fasaha, da kaya a matakin duniya.
Sanata Shettima ya yi wannan bayani ne a lokacin da Mo Abudu ta kai masa ziyara a fadar shugaban ƙasa a ranar Litinin. Ya jaddada cewa ofishinsa zai bayar da cikakken goyon baya ga shirin a dukkan fannoni. Ya kuma yaba da irin gudunmawar da Abudu ke bayarwa wajen bunƙasa masana’antar nishadi a Najeriya, inda ya ce akwai abubuwa da dama masu kyau a ƙasar da ya kamata a gabatar wa duniya.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana shirin Naija Creates a matsayin wata hanya da za ta taimaka wajen cimma ƙudirin gwamnatin Tinubu na faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga. Haka kuma, ya buƙaci Mo Abudu da ta shiga tawagar gwamnatin tarayya ta iDICE, domin amfani da ƙwarewar ta wajen cimma burin gwamnati a ɓangaren fasaha da ƙirkire-ƙirkire.
Tun da farko, Mo Abudu ta bayyana cewa shirin zai taimaka wajen fitar da fasahar Najeriya zuwa duniya, musamman a fannonin fim, kiɗa, kayan kawa, da abinci. Ta ce a lokacin bazarar shekarar 2025, shirin zai fara ne a Birtaniya, inda za a gabatar da haziƙan ‘yan Najeriya a fannoni daban-daban. Haka kuma, ta nemi haɗin gwiwa da goyon bayan gwamnatin tarayya domin tabbatar da nasarar shirin.
