Tinubu ya kafa ‘Polytecnic’ ta Tarayya a Jihar Kano

Spread the love


Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar kafa sabuwar makarantar fasaha a Jihar Kano mai suna Federal Polytecnic a Rano da ke Kudancin Kano.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godwill Akpabio, a yayin zaman majalisar na ranar Laraba.

Ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya kuma saka hannu kan dokar kafa Jami’ar Tarayya ta Kimiyya a Tsafe da ke Jihar Zamfara.

By ukarofi