Mutane da dama sun rasa rayukansu yayin fashewar tankokin fetur biyu a Adamawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A jiya Talata ne wasu tankokin man fetur guda biyu suka kama da wuta a gidan MRS dake kan hanyar Numan kusa da Filin jiragen sama na Yola, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Lamarin da ya haifar da cinkoson ababen hawa a hanyar zuwa Yola, Babban Birnin jihar.

Tuni dai jama’a da dama suka garzaya wajen da abin ya faru don gani da ido ba tare da la’akari da haɗarin da ke tattare da zuwa wajen ba a yayin da tankokin suke ci da wuta.

Haka kuma jami’an kashe gobara daga Hukumar Kashe gobara ta Ƙasa da wasu daga ‘American University of Nigeria’ suka kai ɗauki domin kashe wutar.

Wani shaida ya bayyana wa manema labarai cewa, lamarin ya auku ne a lokacin da wata tanka ke sauke fetur, wanda ya yi sanadiyyar ƙone motoci da dama.

An kuma yi fargabar wutar ka iya yaɗuwa a yankin wanda ke da gidajen mai sama da goma.

Lamarin da ya haifar da asarar dukiyoyi masu yawa, kamar yadda wani shaida ya bayyana.

By Babaji